Jamila Sulaiman
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yaba da ƙoƙarin da wasu bayin Allah ke yi wajen tabbatar da dorewar zumunci a tsakanin su.
Shugaban sashen kula da walwala na hukumar, Malam Salisu Ali Gwale, ya yi kira ga al’umma da su kasance masu riƙo da zumunci tare da inganta hulɗa a tsakaninsu domin samun yardar Allah.
Ya yi wannan kira ne yayin wani taron zumunci na zuriyar Makama da aka gudanar a garin Ɗanzabuwa da ke ƙaramar hukumar Bichi a jihar Kano State.
A cikin jawabin nasa, Malam Salisu Ali Gwale ya yi bayani mai tsawo kan falalar zumunci, inda ya jaddada cewa akwai sakamako mai tsanani ga masu watsi da shi. Ya kuma ja hankalin al’umma da su yi zumunci saboda Allah.
Ya ƙara da cewa, Ubangiji da kansa ya yi alƙawarin fushinsa ga duk wanda ya ƙi yin zumunci.
A nata jawabin, Malama Binta Kafinta, jami’a a hukumar Hisbah kuma ɗaya daga cikin zuriyar Makama, ta jagoranci addu’o’in neman gafara ga iyayen da suka rasu tare da addu’ar fatan kammala taron lafiya.
Wasu daga cikin mahalarta taron, ciki har da Malama Sadiya Isah Musa da Malama Farida Musa, sun bayyana jin daɗinsu kan wannan haɗuwa da aka yi a ƙarƙashin zuriyar Makama.
An gudanar da taron ne a garin Ɗanzabuwa, ƙaramar hukumar Bichi ta jihar Kano, inda ya samu halartar ɗimbin jama’a daga cikin ‘yan uwa da dangi.

