Kungiyoyin ayyukan gaiyya da ke mazabu goma na Karamar Hukumar Tarauni sun sha alwashin ci gaba da yashe magudanan ruwa da kwashe shara da ke toshe hanyoyin ruwa, domin rage barazanar ambaliyar ruwa a lokacin daminar bana.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Ayyukan Gaiyya na Karamar Hukumar Tarauni, Alhaji Ado Salisu Bashir, ya bayyana hakan yayin da kungiyoyin suka gudanar da aikin yashe magudanan ruwa a wasu unguwanni uku da ke Layin Dagaci.
Ado Salisu Bashir ya ce an gudanar da aikin ne bisa la’akari da muhimmancin tsaftace magudanan ruwa kafin da kuma lokacin damina, domin tabbatar da cewa ruwan sama na samun damar gudana ba tare da cikas ba.
Ya bayyana cewa kungiyoyin za su fadada aikin zuwa sauran mazabu da unguwanni na Karamar Hukumar Tarauni, tare da hada kai da al’umma wajen tabbatar da tsaftar muhalli da kare gidaje da hanyoyi daga illar ambaliyar ruwa.
Shugaban ya kuma yi kira ga mazauna Tarauni da su guji zubar da shara a cikin magudanan ruwa, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa toshewar hanyoyin ruwa da kuma ambaliyar ruwa.
Ado Salisu ya bukaci al’umma da su rika tsaftace muhalli akai-akai tare da kai rahoton duk wani magudanar ruwa da ke bukatar kulawa, domin a dauki matakin gaggawa.
Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, da Ma’aikatar Raya Karkara, bisa samar wa kungiyoyin kayan aikin da suke bukata domin ci gaba da gudanar da ayyukan tsaftar muhalli a fadin jihar.
A nasa bangaren, Dagacin Unguwa Uku, Alhaji Mahe Muhammad, ya yabawa kungiyoyin ayyukan gaiyya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi wajen tsaftace muhalli da taimakawa wajen kare lafiyar al’umma.
Ya kara da cewa, aikin yashe magudanan ruwa ba nauyin kungiyoyin ayyukan gaiyya kadai ba ne, don haka ya bukaci dukkan mazauna Karamar Hukumar Tarauni da su hada hannu wajen tabbatar da tsaftataccen muhalli da rage barazanar ambaliyar ruwa a wannan damina.

