Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da warware doguwar takaddamar ƙasa tsakanin Jami’ar Bayero Kano, BUK, da al’ummar Rimin Zakara, wadda ta kwashe kusan shekaru 50 tana haddasa rashin jituwa da tashin hankali.
Gwamnatin ta ce matakin ya samu ne bayan daukar matakan sulhu da tabbatar da adalci ga masu filayen da abin ya shafa.
A wani bayani da aka fitar, an ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce wajen ganin an samar da mafita mai ɗorewa, ciki har da biyan diyya ga masu filaye da kuma biyan kuɗin gine-ginen da ke kan filayen da rikicin ya shafa.
Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na warware rikicin cikin lumana, tare da kare hakkin wadanda abin ya shafa da kuma samar da zaman lafiya tsakanin BUK da al’ummar Rimin Zakara.
Rikicin ƙasar ya dade yana haifar da damuwa tsakanin jami’ar da mazauna yankin, inda gwamnatin jihar ta sha shiga tsakani domin samun mafita mai karɓuwa ga dukkan ɓangarorin.
A shekarar 2025, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai duba takaddamar tare da samar da sabon tsarin shimfidar gidaje da sake tsugunar da mazauna da kuma biyan diyya ga masu kadarorin da abin ya shafa.
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa an samu ci gaba wajen warware rikicin bayan shiga tsakani da gwamnatin jihar, inda aka mayar da hankali kan iyakokin filaye, sake tsugunar da wadanda abin ya shafa da kuma samar da zaman lafiya.
A wani sabon mataki na aiwatar da yarjejeniyar, an gayyaci duk wadanda abin ya shafa kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta tantance su domin halartar taron raba diyya.
An shirya taron ne a Coronation Hall da ke Kano a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, da misalin karfe 10 na safe.
Gwamnatin jihar ta bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen kawo ƙarshen doguwar takaddama da kuma samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin jami’ar da al’ummar da ke makwabtaka da ita.
Ana sa ran biyan diyya da sauran matakan da aka amince da su za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake bullar rikicin a nan gaba.

