Wata Kotun Majistare mai lamba 7 da ke Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali ta yanke hukuncin tura Ashiru Idris, wanda aka fi sani da Maiwushirya, gidan gyaran hali na tsawon makonni biyu, bayan da aka same shi da laifin yada hotuna da bidiyon batsa tare da wata budurwa a kafafen sada zumunta.
Wannan hukunci ya biyo bayan karar da Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta shigar a kansa, bisa zargin karya dokokin hukumar.
Court Orders Investigation into Alleged Affair Involving Sankara
Jami’in yada labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan fitowar su daga kotu.
Ya bayyana cewa matakin kotun ya zama dole domin tabbatar da bin doka da oda, musamman bayan sabunta dokokin hukumar da suka tanadi hukunci ga masu yada abubuwan da ke cin zarafin al’ada da koyarwar addinin Musulunci a kafafen sada zumunta.
“Sabuwar dokar ta baiwa hukumar cikakken iko na sa ido da daukar mataki kan duk wanda ke yada abubuwan da ba su dace ba a kafafen sada zumunta,” in ji Sulaiman.
WOFAN Empowers Kudai Jigawa State with PWDs Center Solar Borehole
Ya kara da cewa hukumar karkashin jagorancin Abba El-Mustapha za ta ci gaba da tsaurara matakai domin dakile yada barna da kare tarbiyyar al’umma, musamman matasa.
A karshe, hukumar ta yi kira ga daukacin al’ummar Kano, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, da su rika bin doka da mutunta al’adun gargajiya da koyarwar addini domin kare mutuncin jama’a.

