Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai koma jam’iyyar APC ba sai an fayyace masa matsayinsa a jam’iyyar kuma sai an dawo da takardun manufofin da suka rubuta kan yadda za a tafiyar da rayuwar talakawan Najeriya.
Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne sai an fayyace masa matsayin magoya bayansa da kuma gwamnatin jihar Kano kafin ya yanke duk wata shawara.
Read also: Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa Bayan Rikici Tsakanin Matuka
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano, yayin da yake karɓar shugabanni da magoya baya daga ƙananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar NNPP.
Read also: Tinubu’s Independence Day Speech Reflects Economic Reform Agenda- Kwankwaso
Jagoran ya bayyana cewa “Idan har zan koma jam’iyyar APC dole ne a sanar da ni matsayi na a cikin jam’iyyar, sai an faɗa mana abubuwan da za a yi mana sannan kuma sai mun san matsayin jihar Kano da magoya bayanmu.”
Kwankwaso ya bayyana cewa burinsa shi ne kare muradun al’umma, musamman talakawa, tare da tabbatar da cewa duk wata tafiya ta siyasa za ta amfanar da magoya baya da kuma jama’ar jihar Kano gaba ɗaya.
Read also: Kebbi APC Rejects ADC Claims of Political Persecution
Wannan furuci na Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
BBC HAUSA

