Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta rubanya ƙoƙari domin tabbatar da cewa dakarunta suna bin dokar da ta kafa hukumar tare da ƙa’idojin aikinta.
Shugaban kwamitin da Hukumar Hisbah ta kafa domin sa ido da gyara ayyukan sassan hukumar a ƙananan hukumomi 44 na jihar, Dr. Jamilu Ajiya Fagge, wanda shi ne Mataimakin Kwamandan Hisbah a sashen horas da dakarun hukumar, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba ayyukan Hisbah a ƙananan hukumomi.
Read also: Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa Bayan Rikici Tsakanin Matuka
Read also: Tarauni Lawmaker Empowers Constituents With 81 Motorcycles
Dr. Ajiya ya ce kwamitin na gudanar da rangadi a faɗin ƙananan hukumomi 44, inda ya zuwa yanzu suka kammala ziyara a ƙananan hukumomi 39, kuma suna sa ran kammala sauran nan ba da daɗewa ba.
Read also: Kebbi Government Hails Army’s New Security Deployments
Ya ƙara da cewa ƙaramar hukumar Tarauni ce ta cika adadin ta 39, inda suka duba ayyukan da dakarun Hisbah ke gudanarwa, tare da ɗaukar matakan da suka dace, sannan za su ci gaba da rangadi a sauran ƙananan hukumomi har zuwa ta 44.
Wakiliyarmu Jamila Sulaiman Aliyu ta rawaito cewa Dr. Jamilu Ajiya yana tare da manyan jami’an hukumar Hisbah daga shalkwatar hukumar a yayin wannan ziyara.

