Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wata muhawara da aka shirya gudanarwa ba tare da izini ba tsakanin Malam Usman Maidubun Isa da Malam Sulaiman Uzair, mai taken “Fadima”, tare da kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan da suka dace domin hana duk wata matsala da ka iya tasowa tsakanin magoya bayan bangarorin biyu.
Hukumar ta jaddada cewa babu wani mutum da ya isa ya take doka, tana mai cewa dole ne a bi ka’idojin da suka dace kafin gudanar da irin wannan taron.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, hukumar ta ce ta samu rahoton sirri kan shirye-shiryen gudanar da muhawarar ba tare da izini ba, wadda ta shafi wani batu mai matukar muhimmanci da ka iya haifar da tashin hankali a jihar, musamman dangane da wakar da ake alakantawa da Nana Fadima da Malam Sulaiman Uzair.
Sanarwar ta kara da cewa shirya irin wannan muhawara a Kano ba tare da hadin gwiwa da Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ko kuma Hukumar Tace Fina-Finai ba, laifi ne mai matukar nauyi da ka iya jawo hukunci bisa doka.
Hukumar ta kuma tunatar da cewa irin wannan lamari ya taba faruwa a baya, inda wata muhawara da aka gudanar ba tare da izini ba ta haifar da rashin fahimta da tashin hankali tsakanin magoya bayan Malam Usman Maidubun Isa da Malam Shehi Maitajul’izzi.
Ta bayyana cewa dokar da ta kafa hukumar ta ba ta ikon sa ido da kula da ayyukan mawakan addinin Musulunci a fadin jihar, tare da jaddada cewa irin wadannan muhawarori marasa tsari na barazana ga zaman lafiya, tsaro da tarbiyyar al’umma.
A saboda haka, hukumar ta yi kira ga mawakan addinin Musulunci da daukacin al’umma da su ci gaba da ba ta hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kuma nasarar ayyukan da take gudanarwa.

