Sani Muhammad
Hukumar Kula da Ilimin Almajiranci da Mayar da Yaran da ba sa Zuwa Makaranta ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta ƙaddamar da sabon shirin inganta tsarin gudanar da makarantun tsangayu da rage yawo da barace-baracen almajirai a tituna da unguwanni.
Read also: Kano Ta Rufe Gidajen Wanka Biyu a Kasuwar Sabon Gari
Jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Kano, Alhaji Abubakar Yaro Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a Ƙaramar Hukumar Kiru.
Ya ce ziyarar Kiru na daga cikin matakan ƙarfafa hulɗa da al’umma, musamman malamai masu kula da makarantun tsangayu da iyaye, domin sanar da su sabbin tsare-tsaren hukumar.
A cewarsa, shirin ya fi mayar da hankali kan rage yawan almajirai da ke yawo a tituna da lunguna domin neman abinci, tare da tabbatar da cewa yaran da iyayensu suka kai wajen malamai domin karatu suna samun kulawa da abubuwan da suka dace.
Alhaji Abubakar Yaro Muhammad ya jaddada cewa manufar shirin ba wai hana yara zuwa makarantun tsangayu ba ce, sai dai inganta yanayin karatu da kulawar da ake ba su.
Ya ce shirin zai shafi Jihar Kano da sauran sassan ƙasar nan, inda aka zaɓi Ƙaramar Hukumar Kiru a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da za a fara aiwatar da shi.
Read also: Nijeriya za ta Kara Karfafa hulɗa da Kasar Saudiyya
Ya ƙara da cewa hukumar za ta yi rajistar makarantun tsangayu, malamai, almajirai da gidajen da ke kula da su, tare da haɗin gwiwar al’ummar yankunan.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Sakataren hukumar na ƙasa, Dr. Muhammad Sani Idris, wanda Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Alhaji Nura Muhammad, ya wakilta, ya ce gwamnati na da nauyin tabbatar da kare haƙƙoƙin almajirai da makarantun tsangayu.
Ya ce duk wani tallafi ko kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta aika wa jihohi domin amfanin almajirai da makarantun tsangayu, ya kamata a ware rabon da ya dace domin cimma manufar da aka samar da kuɗaɗen.
Alhaji Nura Muhammad ya kuma yi kira ga iyaye da su ɗauki nauyin kula da lafiyar ’ya’yansu, abinci da suturarsu, yana mai cewa bai dace iyaye su kai yara wajen malamai ba tare da samar da abubuwan da za su taimaka wajen kula da su ba.
Ya ce gwamnati, a nata ɓangaren, tana da alhakin samar da ilimi da sauran muhimman abubuwan more rayuwa, ciki har da ruwan sha da wutar lantarki, domin rashin ilimi, tsaro da kulawar lafiya na iya haifar da manyan matsaloli ga al’umma.
Read also: Kano Seeks Stronger Economic Ties with Saudi Arabia
Shi ma da yake jawabi, Hakimin Kiru, Alhaji Ibrahim Hamza Bayero, Dan Majen Kano, ya yi maraba da shirin, yana mai cewa zai taimaka wajen magance wasu ƙalubalen da ke tattare da tsarin almajiranci da kuma mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin ilimi.
Taron ya samu halartar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kiru, Alhaji Abdullahi Sa’idu Mai Gari; Limamin Masallacin Juma’a na Tahfizul Qur’ani da ke Kiru, Alhaji Suleman Bello Kiru; malamai masu kula da makarantun tsangayu, iyayen yara, hakimai da sauran al’umma.

