Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      I’ll dress elegantly for a week, lady vows as Kano women storm markets

      March 29, 2025

      Dr. Abdullahi Umar Ganduje’s Legacy of Progress and Excellence

      December 25, 2024

      The rise and fall of Faruk Lawan: A lesson in power and intrigues

      December 17, 2024

      Will The Axing of Zakirai Make Education Great In Kano

      December 17, 2024

      Harmattan Brings Boom to Tea, Noodle, Bean Cake Sellers in Kano

      December 15, 2024
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      Bagwai Indigene Uplifts GGSS Kiyawa with Modern Facilities

      May 30, 2025

      Traditional Ruler Tasks Parents On Inculcating Moral Values On Their Children

      May 30, 2025

      Bagwai LG Chairman Empowers Youths with N10M, Vehicles

      May 18, 2025

      Shema Swears in New Executive Council Members in Dutsinma

      May 13, 2025

      Minister Advocates Stronger Female Representation In Politics, Business

      May 31, 2025

      Nigeria Vows Stronger Border Control, Warns Against Sovereignty Breach

      May 30, 2025

      FG Trains 535 Youths in Inaugural Steel Industry Bootcamp

      May 27, 2025

      Minister Inaugurates 12-Member Committee on 753-Unit Estate

      May 27, 2025

      NIPR President Elected Global Alliance Regional Delegate-at-Large

      May 16, 2025

      Just in : Minister Ata Arrives Kazan for 2025 Intl Economic Forum

      May 15, 2025

      Renowned Philanthropist Mrs. Maryam Imoke Yanah Recieves Warrior of Hope Award

      April 27, 2025

      Minister Woos French Investors with Nigeria’s Economic Reforms

      April 11, 2025

      Gov Yusuf Declares Monday Public Holiday to Mourn Kano Athletes

      June 1, 2025

      Speaker Falgore Mourns Death of 21 Athletes in Ghastly Crash

      June 1, 2025

      Tragic Road Accident Claims Lives of 20 Kano State Athletes

      May 31, 2025

      KNSG Applauds Judiciary Over Landmark Ruling on LG Polls

      May 30, 2025
    • Politics

      How Ganduje is strengthening APC’s fortune ahead of 2027

      May 25, 2025

      Prepare for Exit in 2027-Jigawa Gov Tells PDP Lawmakers

      May 19, 2025

      APC North-West Endorses President Tinubu for 2027

      May 18, 2025

      Gauta Club Backs Kano State’s Ban on Live Political Programs

      May 12, 2025

      Kano Lawmaker Zubairu Hamza Massu Dumps NNPP for APC

      May 12, 2025
    • Conflict

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025

      El-Rufai Defends Najaatu Muhammad Against Ribadus Denials

      February 5, 2025

      Tinubu’s Corruption Saga: Najaatu-Ribadu Feud Takes Center Stage

      February 5, 2025

      Kano Inaugurates Committee to Investigate Rimin Zakara Dispute

      February 3, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Zamba: Kotu Ta Daure Mutane 29 Bayan EFCC Ta Damke Su

      May 31, 2025

      Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsofaffin Kansiloli Naira Biliyan 16

      May 29, 2025

      Rashin Tarbiyya a TikTok: KNSG ta Gurfanar Da Matum 4 a Kotu

      May 29, 2025

      Gwamnatin Kano zata yi Ayyukan Alumma Na Sama Da Biliyan 32

      May 20, 2025

      Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano ta Dakatar Da Fina-finai Guda 22

      May 19, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Hausa

    Kwamishinan Lafiya Ya Yabawa K/H Uku Akan Rigakafin Shan Inna

    EditorBy EditorNovember 6, 2024Updated:November 6, 2024No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    IMG 20241105 WA0130

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya nuna gamsuwa da yadda shirin rigakafin shan-inna yake tafiya a ƙananan hukumomin Ajingi, Gaya da Wudil.

    Kwamishinan ya nuna gamsuwar ne a ranar Lahadin da ta gabata jim kaɗan bayan kammala duba aikin a wasu sassa na ƙananan hukumomin.

    Ya ce ya ji daɗi sosai da yadda ya ga jama’a sun karɓi shirin hannu bibiyu, wanda shi ne jigon samun nasarar shirin a yankin, yana mai yaba wa ma’aikatan lafiya na ƙananan hukumomin wajen tabbatar da yi wa dukkanin yaran da suka cancanta rigakafin.

    Ad 4

    Kwamishinan ya jinjina wa shugabancin ƙananan hukumomin saboda kyakkyawan aikin da suka yi na bin tsare-tsare da aiki tare kamar yadda aka tsara tun daga matakin jiha, da kuma yadda suke halartar tarukan nazarin yadda aikin ya gudana a kowace rana.

    Ya ce, “Abin farin ne ganin yadda shugaban ƙaramar hukumar Gaya yake zuwa ko ina a yankin domin tabbatar da an yi wa yaran da suka cancanta rigakafin ba tare da tsallake yaro ko daya ba. Ƙari kan haka, shugaban ƙaramar hukumar yakan bayar da tallafin magunguna da kayayyakin aiki a asibitoci don inganta harkokin lafiya a yankin.

    “Bugu da ƙari, an ga mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Wudil yana kai kawo a lungu da saƙo na yankin domin tabbatar da shirin ya cimma nasara a yankin.

    Ad 3

    Dakta Labaran, wanda Daraktan Daƙile Cututtuka Masu Yaduwa na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Ibrahim Aliyu Gano ya wakilta, ya yaba wa jajircewar hakiman yankunan game da rawar da suke takawa don samun nasarar shirin a matsayinsu na iyayen ƙasa, da kuma yadda suke halartar tarukan duba yadda aikin ya gudana a kowace rana, inda a wasu lokutan suke tura wakilai idan ba za su samu damar zuwa ba.

    Ya buƙaci iyaye da su ci gaba da kai yaransu da suka cancanta cibiyoyin yin rigakafi da aka ware ko kuma su bar ma’aikatan da ke bi gida-gida suna yi wa yaran rigakafin domin a daƙile ɓurɓushin cutar shan-inna da aka fara samu a wasu sassa na jihar nan, don haka akwai buƙatar haɗa hannu wajen tukarar matsalar.

    Daga nan sai kwamishinan ya buƙaci jami’ai masu wayar da kan mutane kan kiwon lafiya a yankunan da su ƙara ƙaimi wajen ilimantar da al’umma su fahimci baƙatar da ake da ita ta su bai wa ma’aikata masu bi gida-gida cikakken haɗin kai domin kuɓutar da yaransu daga wannan cuta mai illa.

    Dakta Labaran ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yadda ya mayar da fannin lafiya ɗaya daga cikin manyan ƙudurorin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko wanda tuni kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Zamba: Kotu Ta Daure Mutane 29 Bayan EFCC Ta Damke Su

    May 31, 2025

    Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsofaffin Kansiloli Naira Biliyan 16

    May 29, 2025

    Rashin Tarbiyya a TikTok: KNSG ta Gurfanar Da Matum 4 a Kotu

    May 29, 2025

    Gwamnatin Kano zata yi Ayyukan Alumma Na Sama Da Biliyan 32

    May 20, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    Kano Declares Eid-El-Kabir Break for Primary, Secondary Schools

    June 1, 2025

    NDLEA Cracks Syndicate Using Hajj Pilgrims as Cocaine Mules

    June 1, 2025

    Gov Yusuf Declares Monday Public Holiday to Mourn Kano Athletes

    June 1, 2025

    Speaker Falgore Mourns Death of 21 Athletes in Ghastly Crash

    June 1, 2025
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.