Sarkin Hausawan Arewacin Afirka kuma Shugaban Gidajen Kasuwar Kantin Kwari, wanda kuma shi ne Shugaban Zauren Kantin Kwari, Mataimakin Shugaban Kungiyar Shugabannin Kasuwanni karkashin jagorancin Barista Junaidu, Mataimakin Shugaban AMATA da kuma Ma’ajin kungiyar Coalition of Market Chairmen a Jihar Kano, Alhaji Amb. Balarabe Tatari ya bukaci mahukunta da su sake nazari kan kudirin hana shigo da tufafi da kayan masaku daga kasashen waje, yana mai gargadin cewa matakin zai yi illa ga tattalin arziki da rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya.
Da yake magana kan batun, ya bayyana cewa harkar kasuwancin kayan sawa (textile) na daga cikin manyan hanyoyin samar da ayyukan yi a Najeriya, inda dubban masu sana’o’i daban-daban ke cin moriyarta, ciki har da masu shigo da kaya, da clearing agents, dillalai manya da kanana, masu shaguna da kuma matan gida.
Ambasada Tatari ya ce yankin Arewa na alfahari da kasuwancin kayan masaku, wanda ya kasance ginshikin tattalin arziki ga al’ummomi da dama tsawon shekaru.
Shugaban yace kuma bayyana damuwarsa kan halin da masana’antun cikin gida suka shiga sakamakon matsalolin tattalin arziki, musamman karancin wutar lantarki da tsadar man fetur.
A cewarsa, kamfanonin masaku da dama kamar Nichemtex, Diamond, Gold Star, Angel da sauran su sun durkushe ko sun daina aiki gaba daya saboda matsalolin samar da makamashi da tsadar gudanar da harkokin kasuwanci.
Tatari, ya ce harkar noman auduga, wadda ita ce ginshikin samar da kayan masaku a cikin gida, ta fuskanci koma baya sosai, lamarin da ke kawo cikas ga yunkurin farfado da masana’antar textile.
Ya kara da cewa kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi da ake sarrafawa a wasu sassan kasar ko kasashen waje, idan aka kawo su Arewa, suna kara tsada saboda yanayin tattalin arzikin da ake ciki.
Ya musanta ikirarin cewa kudirin hana shigo da kayan masaku daga kasashen waje zai taimaka wajen bunkasa noman auduga, yana mai cewa har yanzu ba a samar da muhimman abubuwan da za su tallafa wa masana’antun cikin gida ba.
A cewarsa, tsadar rayuwa ta kara kamari sakamakon hauhawar farashin man fetur da sauran kayayyakin masarufi, wanda ya sanya jama’a cikin mawuyacin hali.
Tatari ya kuma tunatar da yadda a lokutan yakin neman zabe ake rabon kayayyaki kamar atamfofi da taliya ga al’umma, yana mai cewa hakan ya nuna irin muhimmancin wadannan kayayyaki ga rayuwar talakawa.
Don haka, ya yi kira ga gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau da zai bai wa ‘yan kasuwa damar zuba jari da fadada harkokinsu maimakon daukar matakan da za su iya kawo cikas ga kasuwanci.
Ya yi zargin cewa idan aka amince da kudirin, zai iya jefa ‘yan kasuwar Arewa cikin mawuyacin hali tare da durkusar da harkokinsu, kamar yadda ya ce wasu bangarorin noma suka fuskanci kalubale a baya.
A karshe, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma jagororin siyasa daga Kano, ciki har da Sanata Barau I. Jibrin, Sanata Sulaiman Kawu Sumaila da Sanata Rufa’i Sani Hanga, da su saurari ra’ayoyin ‘yan kasuwar Kano tare da la’akari da bukatunsu kafin daukar matsaya kan

