Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zargin kutsawa cikin tattaunawar wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa an tuhumi El-Rufai da laifuka biyar bayan an yi wa tuhumar gyara daga uku zuwa biyar. Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta soke tsohuwar tuhumar tare da ci gaba da sauraron sabuwar.
El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa. Bayan haka, lauyansa ya bukaci a ba shi damar tattaunawa da wanda yake karewa, yana mai cewa yana hannun hukumomin tsaro daban-daban.
Sai dai alkalin kotun ta ce ba ta ga karin bayanin da aka ce an shigar ba, inda ta bukaci lauyan ya bi ka’idojin shigar da takardu yadda ya kamata. Daga bisani, an dakatar da shari’ar domin warware matsalar.
Tun farko, El-Rufai ya bayyana a wata hira da gidan talabijin cewa an saurari kiran wayar Ribadu, inda ya zargi gwamnati da sauraron wayoyin jama’a ba tare da izini ba.
Daily Nigerian Hausa

