Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama fitaccen ɗan TikTok, Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International, bisa zargin wallafa bidiyoyin da ke nuna shi yana runguma, iyo da yin wanka tare da mata.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dr. Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana kamen Ukasha.
Read also: KNSG Receives Minimum Wage Report,to Announce New Wage
A cewarsa, hukumar ta kama ɗan TikTok ɗin mai shekara 27 ne bayan samun bayanan cewa ya shigo Jihar Kano.
Dr. Mujahid ya ce a halin yanzu Ukasha yana hannun hukumar, inda ake gudanar da bincike kan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa.
Ukasha, wanda ɗan asalin birnin Gusau ne a Jihar Zamfara kuma mazaunin Abuja, ya amsa tambayoyi a yayin da yake hannun jami’an Hisbah.
A lokacin tambayoyin, Ukasha ya ce bai san adadin bidiyoyin da ya wallafa tare da mata ba, inda ya bayyana cewa wasu daga cikinsu suna nuna shi yana rawa da mata, riƙe da su ko rungume su.
Ya kuma bayyana cewa a wasu bidiyoyin yana ɗaukar mata a bayansa, yayin da wasu bidiyoyin ke nuna shi yana iyo ko yin wanka tare da ’yan mata.
Ukasha ya ce wasu daga cikin bidiyoyin da ya wallafa sun samu masu kallo sama da miliyan ɗaya, yayin da wasu suka kai miliyan biyu da uku.
Read also: Kebbi Warns Against Sale of Free Fertiliser as Distribution Begins
Da aka tambaye shi yadda yake samun matan da yake fitowa da su a bidiyoyin, ya ce kasancewarsa content creator na sa mata su riƙa bibiyarsa.
Ya kuma ce mahaifiyarsa da wasu mutane sun sha yi masa nasiha kan irin abubuwan da yake wallafawa a kafafen sada zumunta.
A cewarsa, yana sauraron irin waɗannan shawarwari, kuma hakan ya sa ya daina wasu daga cikin abubuwan da yake yi.
Ukasha ya nemi afuwa tare da yin alkawarin cewa ba zai sake yin irin waɗannan bidiyoyi ba. Ya ce tun kafin a kama shi ma yana shirin daina irin wannan salon, saboda yana shirin yin aure.
Lokacin da aka tambaye shi ko zai iya auren ɗaya daga cikin matan da yake fitowa da su a bidiyoyi, ya ce mahaifiyarsa na son ya auri wata ’yar uwarsu da ke gida, wadda ba ta amfani da TikTok.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Dr. Mujahid Aminuddeen, ya ce za a gurfanar da Ukasha a gaban kotu bayan kammala binciken da hukumar ke yi.
Read also: Police Crack Down on Crime: Illegal Weapons Factory Raided
Ya kuma gargadi matasa da su yi amfani da TikTok da sauran kafafen sada zumunta cikin taka-tsantsan, tare da kauce wa abubuwan da suka saba wa tarbiyya da addini.
Bayanan da ke shafin TikTok na UK INTERNATIONAL sun nuna cewa Ukasha na da mabiya dubu 262.8, yana bin shafuka 26, yayin da bidiyoyinsa suka samu jimillar likes miliyan 2.4.

