Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama ‘yan mata takwas da wani matashi kan zargin Yawon Tazubar wadda aka fi sani da “Good Evening”.
Mataimakin Kwamandan Janar na Hukumar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka mika wa manema labarai.
Ya ce wadanda ake zargin, mata takwas da namiji daya, an kama su ne yayin wani aikin musamman na karshen shekara da aka gudanar a daren Juma’a a manyan titunan birnin Kano.
“Hukumar ta, yayin wannan aikin musamman na karshen shekara, ta kai sumame a wasu manyan tituna a birnin, inda ma’aikatanmu suka samu nasarar kama ‘yan mata takwas da wani yaro da ke yin kama da ‘Good Evening’.
Kano Hisbah in Fresh Crackdown on Alcohol
Ya bayyana ayyukan wadanda ake zargin, inda ya ce, “Wannan ‘yan mata kan kasance wadanda masu hannu da shuni ke dauka su kai su wuraren da suke so, su yi wasanni da su sannan su ba su kudi daga N5,000 zuwa N30,000.”
Aminuddeen ya ce ‘yan matan, masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20, sun amsa cewa sun shiga harkar yawon tazubar.
An gudanar da sumamen ne a tituna da dama ciki har da Zoo Road, Banana Zoo Road, Ahmadu Bello Way, Lamido Crescent, Tukur Road, Lodge Road, Nassarawa Hospital Road, Magajin Rumfa Road, Sultan Road Nassarawa, da Audu Bako Way.
Mataimakin Kwamandan-Janaren ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da kai sumamen a irin wadannan wurare domin kama masu karya dokar Shari’a a jihar.
Kano Ta Jaddada Kudurin ta na Tallafawa Hisbah Don Inganta Tsaro
Haka kuma, ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da tarbiyyar ‘ya’yansu mata domin dakile harkar batsa da sauran miyagun dabi’u.
Aminuddeen ya bayyana cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu domin a yi musu shari’a yadda ya kamata.

