Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen inganta ayyukan jami’an Hisbah a fadin jihar, domin tabbatar da cewa ba a bai wa bata-gari damar samun mafaka a unguwanni.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a yayin taron samar da tsaro mai taken “Zaman Lafiya Shine Burin Kowa” wanda ya gudana a dakin taro na Coronation Hall.
A jawabin da kwamishinan harkokin addini, Sheikh Tijjani Sani Auwal, ya gabatar a madadin gwamnan, ya ce dukkan mazabu a Kano na da jami’an Hisbah, don haka gwamnati na sa ran za su ci gaba da taka rawar gani wajen dakile shigowar baragurbi da bata-gari.
Shima Babban Kwamandan Hisbah, Dr. Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya yaba da kokarin jami’an Hisbah wajen gudanar da ayyuka da kuma saukar Alƙur’ani domin tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce babu abin da ya fi sa al’umma kwanciyar hankali kamar zaman lafiya, don haka ya bukaci hadin kai tsakanin malamai, ‘yan siyasa da hukumomin tsaro domin dorewar tsaro a Kano.
A nasa bangaren, Malam Muazzam Ibrahim Mai Bushra, tsohon kwamandan Hisbah, ya yi karin haske kan rawar da shari’a ke takawa wajen samar da zaman lafiya.
Ya ce Kano kasa ce mai albarka da kowa ke son zuwa saboda kwanciyar hankali da arziki, amma hakan ba zai dore ba sai gwamnati ta dage wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa.
Ya kara da cewa hukumar Hisbah ta taka muhimmiyar rawa wajen hana aikata laifuka, dakile tashe-tashe, da kuma hana baragurbi samun kafar yin barna a unguwanni.
Ya bayyana fatan cewa taron mai taken “Zaman Lafiya Shine Burin Kowa” zai kara karfafa ayyukan Hisbah duk da kalubalen da suke fuskanta.
A jawabin wakilin shugaban darikar Qadiriyya, Sheikh Kari Allah Kabara, Farfesa Matabuli Kabara, ya bukaci gwamnati ta kara ma Hisbah karfi domin gano masu aikata miyagun laifuka a unguwanni.
Haka zalika, ya gargadi hukumomi da su guji bin tsarin kasashen waje da ka iya sabawa tsarin addinin Musulunci.
Wakilin kwamishinan ‘yan sanda, CSP Jamilu Muhammad, wanda shi ne jami’in gudanarwa na rundunar ‘yan sanda Kano, ya yabawa hukumar Hisbah bisa irin rawar da take takawa wajen rage matsalolin tsaro a jihar.
A nata bangaren, mataimakiyar kwamandan Hisbah, Dr. Khadija Sagir Sulaiman, ta bukaci mata da su kasance masu hakuri da goyon bayan mazajensu, tare da kula da tarbiyyar yara da yin addu’o’in samun sauki a kan kalubalen da al’umma ke fuskanta.
Taron ya samu halartar hukumomin shari’a da manyan malamai na jihar Kano

