Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Hadejia ta Jihar Jigawa, wadanda suka da hada Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu da Asibitin Wankin Ƙoda, Tituna da kuma Rumbum Tanada Abinci, domin bunƙasa ilimin fasahar zamani, ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya, inganta hanyoyi da kuma tabbatar da wadatar abinci, daidai da manufar Shugaban Ƙasa ta Renewed Hope Agenda.
Cibiyar Fasaha ta Bola Ahmed Tinubu, wadda Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) ta samar, za ta kasance cikakkiyar cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar zamani. Cibiyar ta ƙunshi dakin bincike na zamani (FabLab) don nazarin basirar AI, na’urorin mutum-mutumi (Robotics) da fasahar kiwon lafiya, tare da cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire mai amfani da AI da kuma habaka kamfanoni masu tasowa (Startup Incubation Centre). Har ila yau, an tanadi dakunan jarabawar kwamfuta (CBT), wuraren aiki na haɗin gwiwa, babban zauren taro na zamani da kuma masaukin ɗalibai mai ɗaukar mutane 60.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma ƙaddamar da Asibitin Sanata Oluremi Tinubu da Cibiyar Wankin Koda, wanda aka gina domin girmama ta, kuma gidauniyar FutureMap Foundation tare da eHealth Africa suka gina tare da cikakken kayan aikin likitanci na zamani, ciki har da na’urorin gwaje-gwaje da wankin koda, domin faɗaɗa samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummomin da ba su samun da isasshiyar kulawa.
7-Year-Old Donates Savings to Oluremi Tinubu Education Fund
Domin tabbatar da ci gaba da samar da ingantattun ayyukan lafiya, asibitin ya haɗa da dakunan gwaje-gwaje na zamani, cibiyar wankin koda, dakin tiyata da kuma sashen kula da mata masu juna biyu da haihuwa. Haka kuma, an tanadi tsarin samar da iskar shaka (oxygen) na zamani, yayin da cibiyar ke amfani da makamashi mai sabuntawa domin tabbatar da cewa babu katsewar ayyukan lafiya.
Da take jawabi yayin ƙaddamarwar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta buƙaci matasa da su yi amfani da damar da cibiyar ke bayarwa domin ba da gudummawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fasahar zamani. Ta kuma yabawa Darakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da cewa al’ummomi a faɗin ƙasar nan suna cin moriyar fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.
Kano to Host National Launch as FG Unveils ECoN Initiative
Ƙaddamarwar ta kasance wani ɓangare na ziyarar farko da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai Jihar Jigawa, inda ta kuma ƙaddamar da Shirin Rumbum Abinci na Ƙasa na Yankin Arewa maso Yamma, tare da buɗe wasu muhimman ayyukan more rayuwa, ciki har da Titin Bola Ahmed da Titin Oluremi Tinubu, wanda hakan ke ƙara nuna jajircewar gwamnatin Renewed Hope wajen faɗaɗa damar samun fasahar zamani, ingantaccen kiwon lafiya da ci gaban ƙasa mai haɗa kowa da kowa.
Hausa Daily Times

