Al’ummomin kudu maso gabas da kudu maso kudancin Nijeriya da ke zaune a Jihar Kano sun tabbatar wa gwamnatin jihar cewa za su ba da dukkan gudunmawarsu domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da ci gaban jihar a dukkan fannoni.
Wannan tabbaci ya fito ne yayin wani taron tattaunawa na musamman da masu ruwa da tsaki, wanda ya haɗa shugabannin al’ummomin kudancin ƙasar nan mazauna Kano, domin duba hanyoyin da za su taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kwanciyar hankali a jihar.
Taron wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano ta shirya, ya gudana ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ma’aikatar, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya.
Da yake jawabi kan manufar taron, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa Jihar Kano jiha ce mai karɓar kowa da kowa, wadda ke ba da kulawa da kariya ga dukkan al’ummomin da ke zaune a cikinta ba tare da nuna bambanci ba.
Kwamred Waiya ya Kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin jihar Karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf take yi wajen ganin ta magance matsalolin tsaro da suka faru a wadansu kananan hukumomin dake jihar.
Ya ce gwamnatin ta dauki dukannin matakan da su ka dace wajen ganin ta inganta harkokin tsaro a Kananan hukumomin Bagwai da Shanono ciki har da gudanar da taron addu’oi.
“Ina kira a gare ku da ku gudanar da addu’oin dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a coci coci yayin bikin kirsimeti domin Cigaban jihar Kano”
Ya kuma buƙaci shugabannin al’ummomin kudancin ƙasar nan da su taimaka wajen karyata jita-jita da labaran ƙarya da ake yaɗawa a wasu jihohi, musamman rahotannin da ke nuna cewa Kano ba ta da tsaro, yana mai jaddada cewa irin waɗannan bayanai na ƙarya na iya haifar da tashin hankali da rashin fahimta.
“Kano ita ce jihar da tafi kiwacce jiha zaman lafiya da tsaro Kuma Gwamnati zata cigaba da zage damtse wajen ganin al’ummar ta sun kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ”
A nasa jawabin, Sarkin al’ummar Edo mazauna Jihar Kano, Wanda Kuma shine jagiran tawagar a yayin ziyarar Chief Fred Akhigbe, ya tabbatar da cewa al’ummomin kudu maso gabas da kudu maso kudancin ƙasar nan za su ci gaba da ba gwamnatin Kano cikakken goyon baya wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
Ya ƙara da cewa al’ummomin su na zaune lafiya da juna a Kano, kuma a shirye suke su haɗa kai da hukumomin gwamnati da na tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Taron ya samu halartar shugabanni da wakilan al’ummomin kudu maso gabas da kudu maso kudancin Nijeriya mazauna Jihar Kano wadanda suka hada da Bayelsa,Rivers,Cross Rivers,Delta da Edo, wanda suka jaddada muhimmancin haɗin kai, fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.

