Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an bi dukkan ka’idojin shari’a yadda doka ta tanada a hukuncin da aka yanke kan Victor Solomon, tare da karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa akwai sabani ko rashin adalci a hukuncin.
Kwamishinan Shari’a na jihar, James A. Kanyip, ya bayyana hakan yayin da yake karin haske kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke a ranar 6 ga Janairu, 2026. Ya ce Solomon ya fuskanci shari’u guda biyu mabambanta a gaban kotuna daban-daban, kan laifuffuka da suka shafi mutane daban.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, Kanyip ya ce:
“Babu wani sabani a hukuncin da ake yadawa a kafafen sada zumunta. An gurfanar da Victor Solomon a shari’u biyu ne daban. A shari’a ta farko an wanke shi a shekarar 2024, amma a shari’a ta biyu an same shi da laifi a 2026 bisa kwararan shaidu.”
Ya yi bayanin cewa shari’ar farko mai lamba KDH/KAD/73C/2020, wadda ta shafi zargin hada baki da yunƙurin aikata kisan kai, ta kare da wanke shi a ranar 21 ga Mayu, 2024.
Sai dai a shari’a ta biyu mai lamba KDH/KAD/78C/202, wadda ta kunshi manyan laifuffuka da suka hada da hada baki, jikkata mutum ba tare da dalili ba, da kuma kisan kai, kotu ta same shi da laifi bayan kammala sauraro a watan Oktoban 2025. Daga bisani aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 6 ga Janairu, 2026.
“Kotu ba ta yanke hukunci bisa son rai ko siyasa ba. An gudanar da cikakkiyar shari’a, alkalai sun tantance dukkan hujjoji bisa gaskiya da doka,” in ji Kanyip.
Ya kuma kara da cewa wanda aka yanke wa hukuncin yana da cikakken ‘yancin daukaka kara har zuwa Kotun Koli, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.
Shi ma Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ya gargadi jama’a kan yada labaran karya musamman kan batutuwan shari’a.
“Yada labaran karya game da hukuncin kotu abu ne mai hatsari. Yana iya tayar da hankalin jama’a da haddasa rikici ba tare da dalili ba. Muna kira ga al’ummar Kaduna su rika tantance sahihancin labari kafin yadawa,” in ji Maiyaki.
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na kare gaskiya da tabbatar da adalci ga kowa, tare da bukatar jama’a su dogara da bayanan hukuma maimakon jita-jita.

