Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Shanu da Dillalan su da Masu Sarrafa su a Kano, Alhaji Usman Usman Fulani, ya bayyana cewa inganta kasuwannin dabbobi wato Kara a fadin jihar hanya ce ta bunkasa tattalin arziki.
Fulani ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar a Karamar Hukumar Dambatta, inda ya jaddada muhimmancin rawar da kungiyar ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da bunkasa tattalin arzikin jiha da na kananan hukumomi musamman ta fannin samar da kudaden shiga.
Ya kara da cewa kaddamar da shugabannin wannan kungiya zai taimaka wajen kara darajar kasuwannin dabbobi, da kuma yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da duk masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwancin shanu da safarsu da sarrafasu daga jiha zuwa jiha.
Shugaban kungiyar ya bukaci Karamar Hukumar Dambatta da ta samar da tallafi wajen gyaran kasuwar dabbobi, ciki har da samar da bandakuna, tsaro mai inganci, da gidajen kwana da wanka, domin tabbatar da kasuwar na cigaba da zama wuri mai kima a harkokin sayar da shanu.
A jawabin sa, Jami’in cibiyar L-Press, Abubakar Muhammad Kabir, ya sha alwashin ganin kasuwar ta samu tagomashin kayayyakin more rayuwa domin inganta kasuwancin shanun da safararsu da sarrafasu, inda ya ja kunnuwan shugabannin su rike gaskiya da adalci a jagorancinsu.
Haka zalika, Tijjani Ibrahim Zakari, jami’i mai kula da Kano ta Arewa na kungiyar, ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da hada kan ‘yan kasuwa masu mu’amala da saye da sayar da shanu domin bunkasa yankin, tare da kira ga masu ruwa da tsaki a Dambatta da su tallafawa kungiyar.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Dambatta, Sadiq Fagwalawa, ya jaddada goyon bayan hukumar ga kungiyar, inda ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a kawo dauki domin gyara kasuwar shanu.
Hakimin Dambatta, Sarkin Ban Kano, Dr. Mansur Dr. Muktar Adnan, wanda wakilinsa Baba Ado ya halarci taron, ya yi fatan shugabannin kungiyar za su guji duk wani abu da zai iya rage daraja ko mutuncin kungiyar ko na karamar hukumar, tare da jaddada bukatar yin adalci tsakanin ‘yan kasuwa, musamman wajen baiwa bako fifiko.
Sabon Shugaban Kungiyar na Dambatta, Muktar Dahiru Ibrahim, ya sha alwashin gudanar da shugabanci cikin gaskiya da adalci tare da bin dokokin kungiyar a kowane lokaci. Ya kuma roki hadin kan ‘ya’yan kungiyar domin ci gaban kungiyar da karamar hukumar baki daya.
A yayin taron, an kaddamar da katin shaida na kungiyar da kundin gudanarwa da sauran abubuwan da suka shafi shugabanci da gudanarwa.

