Ahmad Muhammad
Dan takarar neman zama Gwamna Jahar Kano a karkashin Jamiyyar ceton talakawa ta NDC, bisa Jagorancin Shugaban Kwankwasiyya na Duniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Tun daga dawawar mulkin Dimocradiyya a shekarar Alif Dari tara da casain da tara 1999 sunan Comrade Aminu Abdussalam a fagen siyasar jahar Kano, ba bako bane, a dukkanin gidajen siyasa da suka rage a wannan lokacin.
NDC Unveils Political Heavyweight Gwarzo for Kano Governorship Race
Kodayake tun kafin wannan lokacin, ya sha gwagwarmayar siyasar kungiyoyin kwadago kama daga matakin karamar hukumarsa, jihar Kano, da Arewa maso yamma, kai da Kuma Nigeria baki daya.
Jajircewarsa a fagagen wadannan mukamai da iya jagoranci da kokarin sa wajen kwato hakkin mai hakki ta hanyar tunkarar duk wani Shugaba mara adalci ya jawo masa farin jinin da har ta kai shi ga rike shugabancin karamar hukumar Gwarzo tun ma kafin 1999.
Zamu kawo kadan daga cikin bayanai dangane da wasu mukamai da Dan takarar Gwamna a Jam, iyyar NDC ya rike, wanda suka sanya shi zama wata dan daren goma 14, wanda talakawa da sauran Alummar jihar Kano suka dade suna godon ya jagorance su a kujera mafi daraja da karamci wato kujerar Gwamna.
Dan Amanar Madugu Kuma Dan Masanin akidar Kwankwasiyya, mai tawakkali, da baya wura-wura da dukiyar jamaa, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya rike mukamai kamar haka:
1 Shugaban kungiyar cigaban matasa Gwarzo wato Gwarzo Youth Progressive Association (G.Y.P.A) — falle biyu daga (1993–1994), (1994–1995)
2. Sakatare a hukumar tara Haraji ta jahar Kano wato Kano State Internal Revenue Board. Kuma zababben mai binciken kudi a kungiyar Maikatan jihar Kano State Civil Service union.
3. Daga nan kuma aka ga irin Jajircewarsa aka zabe shi a matsayin shugaban kungiyar ta Kano State Civil Service Union.
4. An Kuma sake zabar sa a matsayin Babban Jamiin Kungiyar maaikata na jahohi 19 na Arewacin Nigeria.
5. An zabi Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin Shugaban karamar hukumar Gwarzo wato a shekarar (27 March 1996 – 12 December 1996)
6. Ya tsaya takarar nema zama Dan Majalisar Taraiya mai wakiltar Gwarzo/Kabo a shekarar (1997)
7. Bayan dawowar mullin Dimocradiyya a shekarar (1999–2002) an sake zabar Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin shugaban karamar hukumar Gwarzo a karkashin Inuwar Jam iyyar PDP.
8. Ya zama shugaban kungiyar Kananan hukumomi ta jahar Kano wato Association of Local Government Chairmen (ALGON), a shekarar (1999–2002).
9. An sake zabarsa a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar Kananan hukumomin ta ALGON na kasa baki daya.
10. Kafin haka Kuma, yama rike Babban jamiin kungiyar ta ALGON mai kula da jahohin a Arewa maso yamma.
11. Kwamishina a hukumar kula da majalisun kada mai suna National Assembly Service Commission a shekarar (2006–2011).
12. A shekara ta 2011 zuwa 2012 ya zama Kwamishina a Maaikatar Sanya ido da Bibiyar aikace-aikacen Gwabnati wato Project Monitoring and Evaluation, Kano State. A karkashin jagorancin Mai girma Gwamnan jahar Kano na wannan lokacin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
13. Kwamishina a Harkokin hada-hadar Gwamnati wato State Affairs, Kano State Government (2012–2015)
14. Shugaban Hukumar gudanarwa ta Kwalejin Taraiya wato, Federal College of Education (F.C.E.) Kontagora (2017–2019)
15. Mataimakin Gwamnan jahar Kano daga ranar (29th May 2023 zuwa 27th March 2026)
16. Kwamishina, Maaikatar Kananan Hukumomi da Masarautun Hargajiya. Ministry of Local Government & Chieftaincy Affairs (2023–2025)
17. Kwamishina, Maaikatar Ilimi mai zurfi a shekara ta (2025–2026).
Tirkashi!!. Idan ka duba kadan daga cikin jerin wadannan mukamai da Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya rike, na wadannan lokutan ai ba sai an fada ba, ka san akwai kwarewar aiki da gogaiya da jamaa tun daga tushe.
Zaman Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a babbar Jamiar siyasa ta darikar Kwankwasiyya, karkashin Jagora Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanya ya kara wata gogewa da nutsuwa ta musamman tare da hakuri da kawaici.
Wajen iya muamala da saukin kai irin na Kwamred, ya janyo masa haiba ta musamman, ta yanda hatta yan Adawa suka jin nauyin sa Kuma suka dauke shi a matsayin Uba.
Wani Mawaki yace a yanzu Kano ta shiga dimuwa da rigingimun daba, taaddanci da rashin tsaro a arewaci, rashin ruwan famfo da tsadar rayuwa, amma Kuma gashi duk watan duniya Gwamnatin jaha na sumbuke miliyoyin daruwan kudade da ake aikowa daga Taraiya amma, baa san ina suke makalewa ba.
Kwankwaso Na Shirin Tsayar da Gwarzo Takarar Gwamnan a Kano
Saboda haka, yanzu ga Dan Gwarzo Dan gwagwarmayar kwatar yancin talkawan jahar Kano, mai dogaro ga Allah Dan Masanin Kwankwasiyya, firgicin butulawa ya futo domin kawo chanji na gaskiya, Kwamred Aminu Abdussalam zai samarda aiyuka, ruwan sha, tsaro, tallafi, farfado da ilimi, taimakawa mata Kananan yara, Tsofaffi da matasa.

