Ahmad Muhammad
Naji kafafan sada zumunta sun dauki dumi sakamakon daukar tsohon Gwamnan jahar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakin dan takarar zama shugaban Kasa a karkashin inuwar jami, iyyar National Democratic Congress (NDC) da Mr. Peter Obi tsohon Gwamnan jahar Anambra.
Wannan bai zo da mamaki ba ganin irin yanda wasu mutane yan jari hujja suka fadi warwas wajen gaza samun nasasar wanke kwakwalen mutane akan wai Kwankwaso shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake wa aiki.
Saboda ba su samu nasara ba, sai suka sake sabon salo na amfani da Arewa ko kuma addini domin bata Kwankwaso, wai ya dauko dan Biyafara.
Idan mai karatu zai iya tunawa irin wannan salon ne wadannan mutane su ka yi amfani dashi a lokacin marigayi General Muhammadu Buhari yana takara, ake kiransa wai yana daukar nauyi yan Boko Haram dan dai a bata shi a Kuma hana shi cin zabe.
Tarihi a kullum Maimaita kan sa yake, domin hada alakar siyasa da yan kudu ko jamiyyar yan kudu, ba daga kan Kwankwaso aka fara ba, ya samo asali ne daga Mallam Aminu Kano.
Tun kafin samun yanci farko shekarar samun yanci, ta Alif dari tara da sittin 1960 Mallam Aminu Kano, Allah ya jikan sa da Rahama ya dauko jamiyyar National Council of Nigeria and the Cameroons, (NCNC) ta su Dr. Nnamdi Azikiwe da jamiyyar Action Group (AG) itama ta mutanen kudu Kuma suka hada alaka mai karfi.
Haka Kuma a shekarar 1953, ya dauko jamiyyar mutanen yamma wato kasar Yarabawa ta su Awolowo da Kuma shekarar 1979, inda ya dauko jamiyyar su Zik ta mutanen Gabas maso kudu wato jahohin Igbo ko Inyamurai.
Kuma aladar hada shugaban Kasa dan Kudu da mataimakin dan Arewa ko Musulmi da Kirista, ko da Arewa da dan Kudu mataimaki, shima ba akan Kwankwaso da Obi aka fara ba.
Me ya sanya na Atiku da Amechi, da Kassim Shettima da Tinubu ba su zama Yaudarar Arewa ba sai na Kwankwaso? Ga marigayi Buhari da Pastor Osinbajo, ga Atiku da Obasanjo ga Alex Ekweme da Shagari.
A tarihi Arewa ita kadai ba ta taba kawo shugaban kasa ba saboda Nigeria ba ta mu ce mu kadai ba, da zaa ce babu wani mai hakki sai yan tsiraru yan wasoso.
Saboda haka, wannan Kamfen na yan jari hujja da yaki fa talakawan Nigeria ba zai je ko ina ba zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
Maimakon a tsaya ayi magana akan matsalolin tsaro da suka addabi dukkanin sassan Arewa sai ake fakewa da maganganu da busu da tushe balle makama.
Wannan yakin siyasa ne tsakanin talakawa dana yan jari hujja, wanda dole alumma su nemarwa kan su mafita a wannan zabe da yake tunkaro Mu, ko kuma a cigaba a cikin wannan hali na rashin imani da azzaluman shugabanni su ka kakaba ma na.
Daga Ahmad Muhammad

