Wasu matasa da suka fusata sun kashe wata mata da ake zargi da satar yara ta hanyar banka mata wuta a garin Marabar Jos da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun dauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar matsalar satar yara da ta dade tana addabar al’ummomin yankin da kewaye.
Wakilin gidan rediyon Nagarta ya ruwaito cewa, tun da misalin karfe 12 na rana ne aka kama matar, inda jami’an ‘yan sanda suka karbe ta domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata.
Sai dai matasan sun ki amincewa da matakin da ‘yan sandan suka dauka, inda suka dage cewa sai an fito da matar da ake zargin ko kuma su kona ofishin ‘yan sandan.
A wani bangare, mijin matar da malaminta a makarantar Islamiya sun yi Allah-wadai da abin da suka bayyana a matsayin danyen aiki da matasan suka aikata.
Sun bayyana cewa matar ta fita ne domin zuwa wata makarantar Islamiya da ake gudanar da wa’azi, kuma kasancewar ba ta san inda makarantar take ba, sai ta rika tambayar mazauna yankin hanya.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammad Rabi’u, tare da Shugaban Karamar Hukumar Igabi, Alhaji Sani Abdul, sun ziyarci garin Marabar Jos domin jajanta wa al’umma tare da duba halin da ake ciki.
Jami’an sun yi alkawarin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin abin da ya faru. Haka kuma, sun bukaci al’umma da su kwantar da hankula tare da kaucewa daukar doka a hannu.
Nagarta Radio

