Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da ma’aikatan wucin gadi 51 na Radio Kano Ma’aikata na dindindin, bayan amincewar Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na cike guraben da ma’aikata suka yi ritaya.
Shugaban gidan Radio Kano, Kwamared Abubakar Adamu Rano, ya bayyana wannan a matsayin gagarumar nasara a tarihin gidan rediyon. Ya kuma miƙa godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Maimota, da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suka bayar wajen tabbatar da wannan nasara.
Mataimakiyar Shugaban Radio Kano, Hajiya Zulaihat Yusuf Aji, tare da Daraktar Mulki da Gudanarwa, Hajiya Nafisa Abdulkadir Magashi, sun shawarci sababbin ma’aikatan da su kasance masu biyayya ga dokoki da ƙa’idojin aikin gwamnati, tare da nuna ƙwazo, jajircewa da riƙon amana.
Shugaban ƙungiyar RATTAWU reshen Jihar Kano, Kwamared Babangida Mahmuda Biyamusu, da Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen Radio Kano, Kwamared Abdulsalam Na’iya Ibrahim Gwammaja, sun yabawa shugabancin Radio Kano bisa mayar da ma’aikatan wucin gadi zuwa aikin dindindin.
Da take jawabi a madadin waɗanda suka amfana, A’isha Ahmad ta bayyana farin cikinsu tare da alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban Radio Kano.
A wajen taron, an kuma karrama Abubakar Balarabe da Nura Isa Ado da Abdulrazak Sagir Makwarari saboda ƙwazo da ƙwarewarsu wajen gudanar da aiki.
Haka kuma, Daraktan Sashen Labarai da Al’amuran Yau da Kullum na Radio Kano, kuma Ma’ajin NUJ reshen Jihar Kano, Kwamared Nura Bala Ajingi, ya isar da saƙon godiya a madadin Shugaban NUJ na Jihar Kano, Kwamared Suleiman Abdullahi Dederi. Ya buƙaci sababbin ma’aikatan da su kiyaye ɗa’a da ƙa’idojin aikin jarida da na aikin gwamnati.
A ƙarshe, ƙungiyoyin NUJ da RATTAWU reshen Radio Kano sun karrama Shugaban Radio Kano, Kwamared Abubakar Adamu Rano, da shaidar girmamawa bisa jajircewarsa wajen inganta walwalar ma’aikata da kuma rawar da ya taka wajen tabbatar da mayar da ma’aikatan aikin dindindin.
Radio Kano

