Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa karo na biyu.
An sake zaɓen Ahmed ne a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar na ƙasa (National Convention) da aka gudanar a Abuja, inda zai jagoranci jam’iyyar na tsawon wa’adin shekaru huɗu.
A taron, jam’iyyar ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC). Daga cikinsu akwai Abba Kawu, mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa; Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu; Dipo Olayokun, sakataren ƙasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na ƙasa.
Sauran waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Ibrahim Muhammad, mataimakin sakataren ƙasa; Bala Mohammed, sakataren tsare-tsare na ƙasa; Ahmed Balewa, ma’aji na ƙasa; Akpan Ekan, sakataren kuɗi na ƙasa; Maryam Yasin, shugabar mata ta ƙasa; Muhammad Musa, shugaban matasa na ƙasa; Magaji Ibrahim, mai ba da shawara kan shari’a na ƙasa; da Mustapha Danhajia, sakataren walwala na ƙasa.
Haka kuma an zaɓi Sadiq Abubakar a matsayin mai binciken kuɗi na ƙasa; Bashir Abacha, jami’in hulɗa na ƙasa; Shehu Bello, mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma; Abubakar Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya; Stanley Ijeh, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Kudu; Ademola Ayaode, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Yamma; Collins Onuoha, mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Gabas; da Abdulrahman Auwal, wakilin masu buƙata ta musamman.
Sauran mataimakan da aka zaɓa sun haɗa da Moses Okoh, mataimakin sakataren tsare-tsare na ƙasa; Solape Olatuboson, mataimakiyar shugabar mata ta ƙasa; Fredrick Mbasi, mataimakin shugaban matasa na ƙasa na ɗaya; Chidiobi Jenny, mataimakin shugaban matasa na ƙasa na biyu; Fatai Batola, mataimakin sakataren walwala na ƙasa; Bush Adomson, mataimakin mai binciken kuɗi na ƙasa; Saleh Bade, mataimakin sakataren kuɗi na ƙasa; da Chubisi Emmanuel, mataimakin ma’aji na ƙasa.
Shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar, Bala Mohammedo, ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa ƙa’ida, tare da bin dokoki da ƙa’idodin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta (INEC).
A nasa jawabin bayan sake zaɓensa, Ajuji Ahmed ya ce jam’iyyar ta samu sabon tsari, an ƙarfafa ta, kuma an mayar da ita babbar mai ruwa da tsaki a tafiyar dimokiraɗiyyar Najeriya.
“Idanun al’umma na kan jam’iyyarmu domin ta nuna hanyar da za a bi wajen samun dimokiraɗiyya mai ɗorewa da ci gaba a ƙasar nan,” in ji shi.
Shi ma tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya zaɓaɓɓun jami’an murna, tare da yi musu kira da su kasance masu ladabi, biyayya da kishin jam’iyyar a dukkan ayyukansu.
Daily Nigerian Hausa

