Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin karɓe motocin aiki kirar Hilux guda biyu da ya baiwa ƙungiyar Kwankwasiyya Scholars Assembly (KSA)
Da ya ke zantawa da DAILY NIGERIAN HAUSA, shugaban kungiyar, Dr. Mansur Hassan ya ce gwamnan ya basu kyautar motocin ne a ranar 22 ga watan Disambar 2025 bayan an rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.
A cewar sa, an samu wannan ci gaba ne bayan an raba gari tsakanin Gwamnan da tsohon mai gidan sa, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hassan ya ce yana tsaka da aiki kawai sai ya ji waya daga hukumar karɓar korafe-korafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano cewa su kai wadannan motoci.
A cewar shugaban, bayan sun je hukumar tare da lauyan ƙungiyar, shugaban hukumar ya shaida musu cewa umarni ne daga ofishin sakataren gwamnatin jiha.
Shugaban ya ƙara da cewa tuni dai a yau su ka maida motar da ke wajen da ga hukumar karɓar korafe-korafe, inda ya kara da cewa sayar kuma yana wajen sakataren kungiyar amma gobe za a mayar da ita ga gwamnatin.
Hassan ya zargi cewa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne saboda shi da sauran mambobin ƙungiyar ba su bi gwamnan Kano ba, su na tare da Kwankwaso.
Daily Nigerian Hausa

