Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, ya ce har yanzu shi ne gwamnan jihar duk da matakan tsige shi da majalisar dokokin jihar ke dauka a kansa da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dauki duk wani mataki da zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar ba.
Read also: Over 50% of children under 5 suffer from stunting in Gombe-UNICEF
Gwamnan ya ce kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babban nauyin gwamnatinsa, yana mai bayyana farin ciki da yadda gasar polo ta gudana lafiya ba tare da wata matsala ba, wanda a cewarsa hujja ce cewa Jihar Rivers tana da tsaro ga mazauna jihar da baki.
Read also: Kano Government to Send Erring Developers to Jail
A baya, majalisar dokokin jihar Rivers ta bukaci babban alkalin Jihar ya kafa kwamitin mutum bakwai domin binciken zargin manyan laifuka da ake yi wa gwamnan da mataimakiyarsa.
Read also: NCAA Issues Aerodrome Certificate for Enugu Airport to FAAN
Fubara ya ce duk da kalubalen siyasa, gwamnatinsa za ta ci gaba da cika alkawurran da ta dauka ga al’ummar Jihar Rivers.
Daily Nigerian Hausa

