Jam’iyyar APC ta lashe kujerun cike gurbi na Majalisar Jiha a Ungogo da Kano Municipal da aka gudanar a ranar Asabar a Jihar Kano, bayan zaɓe da aka yi wanda ya samu ƙarancin masu jefa ƙuri’a da kuma rashin halartar jam’iyyu masu adawa.
A Mazabar Kano Municipal, ɗan takarar APC, Nabil Aliyu Daneji, ya samu kuri’u 7,484 ya lashe kujerar, inda zai wakilci mazabar a Majalisar Jihar Kano.
Babban jami’in da ya jagoranci zaɓen (Returning Officer), Farfesa Ibrahim Tajo Siraj, ya sanar da sakamakon kuma ya tabbatar da zaɓen Daneji.
Haka kuma, a Mazabar Ungogo, ɗan takarar APC, Aminu Sa’ad, ya samu kuri’u 8,975 ya samu nasara. Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, jami’in da ya jagoranci zaɓen a wannan mazaba, ya sanar da zaɓen Sa’ad bayan kammala ƙididdigar ƙuri’u.
Zaɓen cike gurbi ya gudana ba tare da halartar manyan jam’iyyu masu adawa ba, ciki har da Jam’iyyar NNPP (New Nigeria Peoples Party), Jam’iyyar PDP (Peoples Democratic Party), da Jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), waɗanda ba su halarci zaɓen ba.
Komishinan Zaɓe na Jihar na Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Abdu Zango, ya danganta ƙarancin masu jefa ƙuri’a da wasu dalilai da suka haɗa da lokacin gudanar da zaɓen da rashin halartar jam’iyyu da yawa.
An gudanar da zabenna cike gurbi necsakamakon rasuwar ‘yan majalisar da ke wakiltar Ungogo da Kano Municipal Aminu Saadu Ungogo da Sarki Aliyu Daneji.

