Jamila Sulaiman
Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da taron horo na kwanaki biyu ga kimanin ‘yan jarida 100 daga kafafen sadarwa daban-daban a Jihar Jigawa, domin inganta kwarewarsu a fannin jaridanci na dijital.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa taron ya mai da hankali kan amfani da ka’idojin gaskiya da tsarin aiki na jaridanci domin tabbatar da inganci a aikin jarida.
Kano Online Chapel Hosts Workshop to Boost Credibility in Journalism
Waiya ya bukaci mahalarta su yi amfani da ilimin da suka samu a taron wajen ayyukansu na yau da kullum.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kafafen Sadarwa na Online Chapel, Abubakar Abdulkhadir Dan Gambo, ya yi godiya ga baki da mahalarta taron, tare da nuna godiya ta musamman ga wadanda suka bada gudummawa wajen gudanar da horon.
Kano Online Chapel Begins Membership Registration for Digital Media Professionals
Hakazalika, babban Sakataren Ma’aikatar Yada Labarai na Jihar Kano, Alhaji Usman Bello, da Shugaban reshen Kungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya na Jihar Jigawa, Comrade Ismail A. Dutse, sun yi kira ga mahalarta taron da su gode wa Allah da Gwamnatin Kano bisa damar horon, tare da karfafa su da su yi amfani da sabon ilimin da suka samu cikin gaskiya da kwarewa a fagen aikin jarida.

