Jamila Sulaiman Aliyu
Gwamnatin jihar Kano KNSG ta bayyana kudurinta na hadin kai da kafafen yada labaran yanar gizo domin dakile yaduwar labaran bogi da ka iya jefa al’umma cikin rudani.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da wakilan kafafen yada labaran da ke aiki ta yanar gizo.
Ya ce gwamnati ba ta da wani buri face yin aiki kafada da kafada da masu yada labarai na zamani, kasancewar su ne hanya mafi sauri wajen isar da sako ga al’umma.
Ya ce idan kafafen yanar gizo suka yi amfani da alkaluma da bayanan da suka dace wajen gyara al’amura, babu shakka za a samu ci gaba. Haka kuma ya jaddada cewa gwamnati ba ta goyon bayan kirkirar labaran da ba su da tushe ko tabbas.
“Ba mu da niyyar tursasa wa kafafen yada labarai. Gwamnatin Kano tana goyon bayan ku dari bisa dari, amma ba mu goyon bayan yaɗa labarai marasa sahihanci,”
A nasa bangaren, shugaban kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo, Comrade Abubakar Abdulkhadir DanGambo, ya ce kungiyar ba za ta taba mara wa duk wani rubutu da zai jawo tarzoma ba. Ya tabbatar da cewa za su sanya idanu sosai don tabbatar da cewa mambobinsu ba su karya ka’idojin aikin jarida.
Wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar Uba Abdullahi, Salisu Ismail Kabuga, da Ibrahim Yaro Dawakin Tofa sun kara da cewa bin ka’idojin aikin jarida shi ne ginshikin samar da zaman lafiya a cikin al’umma, tare da ba wa baƙi masu ziyartar Kano tabbacin aminci da gaskiyar rahotanni.

