Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ado-Ekiti ta soke zaben fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Ekiti gabanin zaben shekarar 2026.
Kotun ta kuma umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani bisa bin doka da ka’idojin cikin gida na jam’iyyar.
Alkalin kotun, Babs Kuewumi, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata a karar mai lamba FHC/AD/CS/29/2025, wadda Funso Ayeni, dan takarar gwamna, ya shigar kan PDP da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).
Ayeni ya kalubalanci sahihancin zaben fidda gwanin da ya fitar da Wole Oluyede, yana mai cewa jam’iyyar ta “gaza gabatar da sahihin jerin sunayen wakilan doka da na wucin gadi” da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben.
Ya ce rashin gabatar da asalin jerin wakilan ya sabawa ka’idojin PDP da kuma Dokar Zabe, lamarin da ya sanya zaben fidda gwanin ya zama ba shi da inganci.
A cikin hukuncinsa, Kuewumi ya ce yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin bai yi daidai da tanade-tanaden doka da kundin tsarin jam’iyyar ba.
Saboda haka, alkalin ya soke zaben tare da umartar PDP da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna cikin bin doka da ka’idoji. Ya kuma umarci INEC da ta sa ido kan zaben.
Har ila yau, ya ce dole ne a bar dukkan ‘yan takara masu cancanta su shiga sabon zaben domin tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuradiyya a cikin jam’iyyar.
Daily Nigerian Hausa

