Hukumar Zaben Uganda ta sanar da sake zaben shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, lamarin da ya tsawaita mulkinsa zuwa kusan shekaru 40 tun hawansa karagar mulki a 1986.
A cewar hukumar, Museveni, mai shekaru 81, ya samu nasara da kashi 71.65 cikin dari na kuri’un da aka kada, yayin da babban abokin hamayyarsa, jagoran adawa Bobi Wine (Robert Kyagulanyi), ya samu kashi 24.72 cikin dari.
Zaben ya gudana ne cikin yanayi mai cike da tashin hankali, inda rahotanni suka nuna yawaitar jami’an tsaro, rikice-rikice da kuma kama ‘yan adawa.
An kuma rawaito kisan-kai da tsare Bobi Wine a wasu lokuta yayin zaben, lamarin da ya jawo suka daga cikin gida da na kasa da kasa.
Bobi Wine ya yi watsi da sakamakon zaben, yana zargin an tafka magudi da murde tsarin zabe, tare da yin Allah wadai da tashin hankalin da aka yi wa masu zanga-zanga. Ya jaddada ‘yancin ‘yan Uganda na zabar gwamnati da suke so, yana mai cewa a karshe jama’a ne za su yi nasara.
Daily Nigerian Hausa

