Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayar da umarnin bai wa ’ya’yan wasu ’yan majalisar dokokin jihar Kano biyu da suka rasu tikitin takara domin fafatawa a zaɓen cike gurbi na kujerun majalisar dokokin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa ’ya’yan ’yan majalisar da suka rasu sun zama ’yan takarar majalisar dokokin jihar Kano a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP.
Read also: Girls’ Education: Kano SUBEB, AGILE Distribute 11 Laptops
A farkon makon da muke ciki ne, ƴan majalisar jiha, Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo da Sarki Aliyu Daneji suka rasu a Rana daya, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini.
Read also: Kano Boosts Adolescent Healthcare with 743 Facilities
Mai taimaka wa Sanata Kwankwaso ta fannin kafafen yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafin Facebook a yammacin ranar Asabar.
Read also: NMDPRA, Power Ministry Move to Improve Electricity Supply
Majiyoyi daga bangaren iyalan ’yan majalisar da suka rasu, tare da wasu jagororin jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Birnin Kano, suma sun tabbatar wa da Daily Nigerian Hausa wannan mataki.
Daily Nigerian Hausa

