Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar Sarkin Sudan, Zazzau, Alhaji Abubakar Hayyat Bambale.
Marigayi Sarkin Sudan ya rasu da yammacin yau a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika, Zaria, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Ya bar matan aure, ‘ya’ya da jikoki da dama. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Malam Yusuf Abubakar Hayyat, Magatakardan Zazzau kuma Sakataren Majalisar Masarautar Zazzau.
Za a gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Abubakar Hayyat bayan Sallan Isha’i a Bambale, Zaria.

