Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta shirya wani taro na musamman da ya zama sanadin sauyin rayuwa ga wasu matasa uku da suka fito daga bangaren nishaɗi, inda suka karɓi addinin Musulunci bayan bayyana ra’ayinsu na rungumar addinin da kansu.
Taron, wanda aka gudanar a harabar dakin taro na Hukumar, ya gudana cikin yanayi na natsuwa da farin ciki, inda Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya jagoranci karɓar Musuluncin matasan a hukumance.
A yayin jawabinsa, Abba El-Mustapha ya bayyana wannan rana a matsayin ɗaya daga cikin ranaku mafi muhimmanci da farin ciki a rayuwarsa. Ya ce shawarar da matasan suka yanke ta samo asali ne daga kyawawan halaye, zaman lafiya, da kyakkyawar mu’amala da suka gani daga abokan sana’arsu Musulmi a cikin masana’antar nishaɗi.
Ya ƙara da cewa irin ɗabi’u nagari da haɗin kai da ake nunawa a tsakanin jama’a sun yi matuƙar tasiri wajen ƙarfafa matasan zuwa wannan sabon mataki na rayuwa.
Matan ukun Dicson da Zara daga Adamawa State, da Hannatu daga Gombe State sun bayyana cewa sun shafe lokaci a Kano suna gudanar da sana’ar su ta nishaɗi kafin daga bisani su yanke shawarar karɓar addinin Musulunci.
Sun kuma nuna godiya ga irin tarbar da suka samu daga jama’ar Kano, inda suka ce kyakkyawar mu’amala, soyayya da mutunci da aka nuna musu sun taka muhimmiyar rawa wajen sauyin da suka yi a rayuwarsu.
Da take magana a madadin su, Hannatu ta bayyana cewa fahimtar da suka samu game da Musulunci a matsayin addinin zaman lafiya, ƙaunar juna da kyakkyawar mu’amala da mutane ba tare da bambanci ba, ita ce ta fi tasiri wajen yanke wannan muhimmiyar shawara.
A cewarta, wannan fahimta ta kasance ginshiƙi mai ƙarfi da ya jagoranci zukatansu zuwa ga rungumar addinin Musulunci.
Taron ya kammala cikin addu’o’i da taya murna ga sabbin mabiya addinin Musulunci, yayin da mahalarta suka bayyana fatan alheri ga sabuwar tafiyar rayuwarsu.

