Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa Malam Usman Aliyu, mijin marigayiya Ummulkhairi malamar Islamiyyar da aka ƙona kyautar gida domin taimaka masa ya sake gina rayuwarsa bayan wannan ibtila’i.
An ƙona matar ne a wani hari da wasu matasa suka kai mata bayan zarginta da satar yara a Maraban Jos da ke jihar.
Read also: Waiya Launches Community Orientation Volunteers Project
Sultan Condemns Mob Lynching of Ummulkhair, Demands Justice
Gwamnan ya miƙa masa takardun gidan ne a lokacin da ya kai masa ziyarar godiya tare da rakiyar Sheikh Haliru Maraya.
Read also: NDC Unveils Political Heavyweight Gwarzo for Kano Governorship Race
Gwamnan ya ce tun bayan aukuwar lamarin, ya kai ziyara ga iyalan marigayiyar domin jajanta musu tare da tabbatar musu cewa gwamnatin jihar ba za ta tsaya ga kalaman ta’aziyya kawai ba.
Kaduna Govt to Sponsor Children of Late Ummulkhairi
Read also: United Athletics Series Ends in Lagos
Ya ce baya ga samar musu da gida da tallafin kuɗi, gwamnati ta kuma ɗauki nauyin karatun ‘ya’yansu domin tabbatar da kyakkyawar makomarsu.
BBC HAUSA

