An shiga sabon rikicin shari’a kan batun cike gurbin mataimakin gwamnan Jihar Kano, inda aka bukaci majalisar dokokin jihar Kano da ta dakatar da duk wani yunkuri na tantance Murtala Garo domin naɗa shi mukamin, har sai kotu ta yanke hukunci.
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 15 ga Afrilu, 2026, wadda aka aikawa Kakakin Majalisar, Jibrin Falgore, lauyoyi daga kamfanin Suleiman Mohammed & Co. sun bayyana cewa sun shigar da kara a madadin Kuliyya Muhammad Salihu da wasu mutum biyu.
Lauyoyin sun ce karar da aka shigar tana kalubalantar yunkurin tantance Murtala Garo domin nada shi mataimakin gwamna, kuma tana gaban Babbar Kotun Jihar Kano.
An bayyana cewa karar mai lamba K/360/2026 ana ci gaba da sauraron ta a kotu, , wato yana gaban kotu, wanda hakan ke nufin bai dace majalisa ta ci gaba da daukar wani mataki ba har sai an kammala shari’ar.
Lauyoyin sun gargadi majalisar da ta dakatar da duk wani aiki da ya shafi batun, suna mai cewa duk wani mataki da aka dauka yayin da shari’ar ke gudana na iya kawo cikas ga tsarin shari’a.
An kuma aika kwafin wasikar zuwa ofishin magatakardar majalisar, kuma an tabbatar da cewa majalisar ta karbi takardar.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da takaddama a siyasance kan kujerar mataimakin gwamna a Kano, inda rahotanni ke nuna cewa ana ci gaba da tuntuba da neman goyon baya daga bangarori daban-daban.
Sabuwar shari’ar dai ta kara jefa sabon salo cikin rikicin siyasar da ke gudana a jihar.
Daily Nigerian Hausa

