Kusan shekaru uku bayan rasuwar fitaccen mawaki Mohbad, har yanzu ba a binne gawarsa ba sakamakon rikici kan gwajin DNA domin tabbatar da dangantakarsa da yaron da ake kira Liam.
Jaridar Premium Times ta rawaito mahaifin marigayin, Joseph Aloba, ya dage cewa dole ne a gudanar da gwajin DNA kafin a kai ga binne ɗansa.
Read also: Gov Abdulrazaq lays wreath, Hails Fallen Heroes at Armed Forces Remembrance Day
Ya bayyana cewa yana son a tabbatar da gaskiyar ko yaron jininsa ne kafin a ɗauki mataki na gaba.
Read also: Tarauni LGA Pledges Support for Community Development Groups
Haka kuma, ya nemi taimakon shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya zargi cewa an samu matsaloli a kotu da kuma yadda ake tafiyar da shari’ar lamarin.
Aloba ya kuma yi zargin cewa akwai wasu da ke hana gudanar da gwajin DNA yadda ya kamata, lamarin da ya jawo tsaiko wajen kammala bincike da kuma binne marigayin.
Read also: Olawande, Fashola, Others to Headline Maiden Nigeria Reputation Summit
A takaice, rikicin iyali da kuma batun gwajin DNA ne suka zama babban dalilin da ya hana a kammala shari’ar da kuma binne Mohbad har zuwa yanzu.
Daily Nigerian Hausa

