Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC za ta fara kokarin cimma matsaya (consensus) wajen fitar da dan takarar shugaban kasa na 2027, amma idan hakan bai yiwu ba za a gudanar da zaben fidda gwani.
Atiku ya kuma ce zai goyi bayan duk wanda ya lashe zaben, yana mai nuna shirinsa na janyewa idan wani ya fi dacewa. Ya kara da cewa zaben 2027 zai zama na karshe a rayuwarsa ta siyasa, inda ya tabbatar ba zai sake neman wani mukami ba bayan wannan lokaci.
A wata hira da ya yi da ARISE TV, ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin masu jagorantar hadakar siyasa domin tunkarar zaben 2027, yana mai cewa hadin kai tsakanin jam’iyyu shi ne mafita.
Sai dai ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa ba ta cika alkawarin da ta yi wa ‘yan kasa ba, tare da gargadin hadarin taruwar iko a hannun bangaren zartarwa.
Atiku ya kuma jaddada muhimmancin kwarewa a shugabanci, yana mai cewa matasa na bukatar gogewa domin su iya tafiyar da mulki yadda ya kamata.
Daily Nigerian Hausa

