Tsohon ministan sadarwa na Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya taɓa mayar da akwatin zaɓensa zuwa Abuja daga Gombe.
A hirarsa da gidan talabijin na TVC a yau Lahadi, Pantami wanda ɗaya ne daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027, ya kuma yi tsokaci kan zargin da ake masa na watsi da lamuran jam’iyyar ta APC na tsawon lokaci.
Pantami ya ce ya maida akwatin zaɓensa zuwa Abuja ne a shekarar 2019 saboda muƙamin da ya riƙe na shugaban hukumar NITDA a lokacin, kuma yana daga cikin masu jagorantar abubuwan da suka shafi bayanan intanet da suke da alaƙa da zaɓen, wanda hakan ya sa ake buƙatar kasancewrasa a birnin tarayyar ƙasar.
Amma ya ce yanzu haka ya maida akwatin zaɓensa jihar Gombe.
A ƴan kwanakin nan dai Pantami ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya, tun bayan da jam’iyyarsa ta APC ta amince da miƙa tikitin takarar gwamnan jihar Gombe ga Jamilu Isiyaku Gwamna bisa tsarin masalaha, abin da Farfesan ya yi watsi da shi, inda ya ce zai yaƙi “rashin adalcin da aka yi”.
Da aka tambaye shi game da rashin ba da gudummuwa ga harkokin jam’iyyar APC a lokacin da yake riƙe da muƙamin minista, Pantami ya ce ba haka batun yake ba.
Ya ce ya sha bayar da gudummuwar kuɗi ga jam’iyyar a lokuta daban-daban, inda ya yi iƙirarin cewa ko a kwanan nan ya ba da “gudummuwar naira miliyan 50” a yayin babban taron jam’iyar a Abuja, da kuma wata “miliyan 45” a lokacin sabunta rijistar jam’iyyar ta APC.
Shehin Malamin ya ƙara da cewa, ba a taɓa neman wata gudummuwa daga gareshi ya ƙi yi ba.
BBC HAUSA

