Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      I’ll dress elegantly for a week, lady vows as Kano women storm markets

      March 29, 2025

      Dr. Abdullahi Umar Ganduje’s Legacy of Progress and Excellence

      December 25, 2024

      The rise and fall of Faruk Lawan: A lesson in power and intrigues

      December 17, 2024

      Will The Axing of Zakirai Make Education Great In Kano

      December 17, 2024

      Harmattan Brings Boom to Tea, Noodle, Bean Cake Sellers in Kano

      December 15, 2024
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      One Confirmed Dead, Woman Rescued Alive in Kano Well Accidents

      June 30, 2025

      Philanthropist Donates 600 Bags of Maize To Insurgency Victims

      June 27, 2025

      Kazaure NDLEA Holds Road Show to Combat Drug Abuse Illicit, Trafficking

      June 26, 2025

      MfLGCA, PACE Partner for Grassroots Governance Reforms

      June 23, 2025

      NAPTIP, NARTO Unveil Strategic Collaboration to Disrupt Trafficking

      July 2, 2025

      Presidency Debunks Rumours of SGF Akume’s Removal

      June 30, 2025

      President Tinubu Embarks on Diplomatic Visit to Saint Lucia, Brazil

      June 28, 2025

      Efficient Civil Service Key to National Development – Alake

      June 25, 2025

      Brussels: Nigeria’s Digital Blueprint Takes Global Stage at IGF

      June 27, 2025

      Nigeria, S/Arabia Sign Agreement to Tackle Smuggling, Boost Trade

      June 27, 2025

      Nigeria Showcases Bold Health Reforms at BRICS, Pledges $200M

      June 19, 2025

      KSrelief to Tackle Nigeria’s Water Shortage with 78 Solar Boreholes

      June 19, 2025

      Jigawa Renames Ministry, Approves N19.6B for 560 Mass Housing

      June 27, 2025

      KNSG Declares Thursday, Work-Free Day to Mark Islamic New Year

      June 25, 2025

      Gov. Yusuf Vows to Empower Media Practitioners in Kano

      June 25, 2025

      Gov Yusuf Condemns Killing of Two Kano Indigenes in Makurdi

      June 24, 2025
    • Politics

      Kano APC Coalition Submits letter to Natl Ag. Chairman, Demands Dissolution Of State Leadership

      July 2, 2025

      “Kwankwaso Remains Our Focus” – Jigawa NNPP Leader

      June 28, 2025

      Breaking: APC National Chairman Abdullahi Ganduje Resigns

      June 27, 2025

      Rivers: Tinubu Brokers Peace in Closed-Door Abuja Meeting

      June 27, 2025

      Radda Dismisses VP Ambition Rumors, Reaffirms Commitment to Katsina

      June 27, 2025
    • Conflict

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025

      El-Rufai Defends Najaatu Muhammad Against Ribadus Denials

      February 5, 2025

      Tinubu’s Corruption Saga: Najaatu-Ribadu Feud Takes Center Stage

      February 5, 2025

      Kano Inaugurates Committee to Investigate Rimin Zakara Dispute

      February 3, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

      July 3, 2025

      Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

      July 3, 2025

      An kwantar da Tsohon Shugaban Kasa Buhari a ICU a Landan

      July 2, 2025

      Sanata David Mark ya fice daga jam’iyyar PDP

      July 2, 2025

      Kano Za Ta Hada Gwiwa da Kungiyoyi Don Rage Talauci — Kibiya

      July 2, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Hausa

    Menene Tasirin Kafa Rundunar Tsaro Ta Jihar Kano?

    EditorBy EditorJanuary 30, 2025Updated:January 30, 2025No Comments5 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    FB IMG 1725344271069

    Tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta sanar da yi wa ƙudurin kafa rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta aike mata karatu na biyu, masana ke ta faman tsokaci dangane da hanyoyin da ya kamata a bi domin samun nasara.

    Turereniyar Karbar Abinci A Coci Ta Yi Sanadiyar Rayukan Mutane 10 A Abuja

    Kano dai na fama da matsaloli irin na rikice-rikicen dabanci da ƙwacen waya, lamarin da ya yi sanadiyar ajalin mutane da dama.

    Ad 4

    Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙiru, Abubakar Tasi’u Ƙiru, na cikin ƴan majalisar da suke goyon bayan ƙudurin, inda ya lissafa wasu abubuwan da ke ƙunshe a cikin ƙudurin kamar haka.

    Ambasada Tatari Ya Mika Godiya Ga Wandanda Suka Halarci Nadin Sarautar Shi

    Kwamanda-Janar na jiha da ƙananan hukumomi ne za su jagoranci rundunar.

    Ad 3

    Jami’an rundunar na da ikon kama masu laifi su hannunta su ga ƴansanda domin gurfanar da su a gaban hukuma.

    Jami’an rundunar na da damar amfani da bindigogi ƙirar gargajiya domin su kare kansu.

    Dakarun za su yi ƙoƙari domin kauce wa shiga harkokin siyasa, domin za a zuba waɗanda ba ƴansiyasa ba.

    Mun Samu Kasuwancin Magunguna na Kano a Rikice -Kwamishina

    Babu wanda za a ɗauka sai an tabbatar da nagartarsa da ingancinsa ba tun daga mahaifarsa, inda a cewarsa masu unguwanni da hakimai za su saka wa mutum hannu kafin a ɗauke shi domin gudun kar a ɗauki ɓatagari.

    A game da wannan yunƙurin na kafa rundunar tsaron, BBC ta tuntuɓi masanin harkokin tsaro, Auwal Bala Durumin Iya, inda ya ce abin farin ciki ne, amma ya kamata a yi abin da ya dace.

    Kwamishina Ya Mayar Wa Gwamnatin Kano Rarar Naira Miliyan Dari

    “Samar da rundunar tsaro ta jihar Kano abu ne mai kyau idan ka kalli irin laifuffukan da ake yi a Kano. Hakan ya sa gwamnati ta ga ya dace ta yi tsarin da ya kamata domin samar da jami’an tsaro da za su taimaka wa jami’an tsaro na gwamnati tarayya domin tabbatar da tsaro a jihar Kano.”

    Ya ce yanzu haka a nasa ɓangaren na masanin harkokin tsaro, yana gudanar da aikin horas da ƴan sa-kai daga ƙananan hukumomin Kano 44 domin koyar da su makamar aiki, domin su san yadda za su gudanar da aikin cikin ƙwarewa.

    A game da batun cewa Kano ba ta fama da barazanar tsaro ta ƴanbindiga, Durumin Iya ya ce kowace jiha na da matsalar da take fuskanta.

    Batagari Sun Yashe Asusun Ajiyar Kudin Wani Dan Kasuwa A Kano

    “Kowace jiha akwai matakin da ya kamata ta ɗauka domin kare ƴan jiharta. Saboda haka Kano na da maƙwabtaka da jihohin da suke fama da matsalolin tsaro, saboda haka ba laifi idan Kano ta ɗauki mataki kafin matsalar ta kawo gare ta. Idan gemun ɗan’uwanka ya kamata da wuta, sai ka shafa wa naka ruwa ne,” in ji shi.

    Sai dai ya ce akwai buƙatar a ɗauki waɗanda suka dace, kuma suke da ƙwarewa aiki da lungu da saƙon jihar.

    A game da fargabar amfani da jami’an tsaron da ake yunƙurin kafawa wajen amfani da su domin muzguna wa abokan hamayya domin cin ribar siyasa, Durumin Iya ya ce komai yana da amfani da rashin amfaninsa.

    MD Radio Kano Yace Sun Samun Nasarori Guda 60 a 2024

    “Amma amfanin samar da rundunar tsaron ya fi rashin amfaninsa. Ai ita gwamnati idan tana so ta yi amfani da jami’an tsaro, har na gwamnatin ma ana amfani da su. Kawai yana da kyau a zaƙulo waɗanda suka dace, sannan a tabbatar sun samu horo yadda ya dace.

    “Ƴan sa-kai su ne suka daɗe suna aikin tsaro. Su ya kamata a ɗauka, a ƙara musu horo bayan wanda muka musu domin a wayar musu da kai kan tsame aikinsu daga siyasa da addini da ƙabilanci da duk wani abu da zai zama cin zarafin ɗan’adam.”

    Ya ce ba za su zama kishiyar ƴansanda ba, kuma a cewarsa, ƴan sa-kai taimaka wa ƴansanda suke yi.

    “Su jami’an tsaron ne za su taimaka wa ƴansanda da bayanan sirri, sannan akwai wurare da dama da ƴansanda ba sa iya shiga, sai ƴan sa-kai ne za su shiga su kamo musu masu laifin su kai musu,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa idan aka samun haɗin kai tsakanin ƴan sa-kai da ƴansanda, lallai za a samu ɗa mai ido.

    Sai dai ya yi kira ga gwamnati da kada ta shigo da ƴansiyasa ciki lamarin, sannan ya yi kira ga ƴan jihar su ba jami’an tsaron goyon baya.

    “Idan aka samu haɗin kai tsakanin mutanen gari da ƴansanda da ƴan sa-kai ɗin, to lallai muna fata matsalolin da ake fuskanta a wasu jihohi ba za su ƙaraso Kano ba. Za a cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci da ibada cikin lumana,” in ji Durumin Iya.

    BBC HAUSA

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

    July 3, 2025

    Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

    July 3, 2025

    An kwantar da Tsohon Shugaban Kasa Buhari a ICU a Landan

    July 2, 2025

    Sanata David Mark ya fice daga jam’iyyar PDP

    July 2, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

    July 3, 2025

    Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

    July 3, 2025

    Barau FC Arrives Asaba for NNL, Targets NPFL Promotion

    July 3, 2025

    Edu Reform in Focus as Kano Partners PLANE for MTSS Workshop

    July 3, 2025
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.