Hukumartaimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) tana ci gaba da aikin tantance masu amfana da shirin kiwon lafiya kyauta (Basic Health Care Provision Fund BHCPF) ta hanyar ziyartar gidaje ɗaya bayan ɗaya.
A yau, aikin ya shiga rana ta biyar tun bayan farawarsa a ranar 6 ga Nuwamba, 2025.
Aikin, wanda zai ɗauki kwanaki 14, yana gudana a ƙananan hukumomi 11 (LGAs) na Jihar Kano, tare da nufin tabbatar da sahihancin bayanai, tabbatar da kasancewar masu amfana a gidajensu, da kuma haɗa su kai tsaye da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko (PHCs da aka ware musu.
KHETFUND Evaluates ₦57.5m Disbursed to KSCHMA for Vulnerable
Wannan mataki, a cewar KSCHMA, yana nuna jajircewar hukumar wajen tabbatar da gaskiya, amana, da cimma burin Kiwon Lafiya ga Kowa (Universal Health Coverage UHC) a Jihar Kano.
Rahotanni daga tawagar masu aikin sun bayyana cewa, zuwa yanzu an ziyarci gidaje 5,365 tare da tantance mutane 8,598, wanda ke nuna kashi 19% na adadin 46,013 da aka shirya tantancewa gaba ɗaya.
Daga cikin waɗanda aka tabbatar, 8,372 an same su a gidajensu yayin ziyarar, 226 kuma ba a same su ba a lokacin.
KSCHMA, CHAI Partner to Strengthen Kano’s Healthcare System
Haka kuma, kusan 97% na masu amfana da aka gani suna da lambar shaida ta ƙasa (NIN) muhimmin mataki wajen tabbatar da sahihancin bayanai da haɗa su da cibiyoyin kiwon lafiya.
A halin yanzu, aikin yana gudana a cibiyoyin lafiya 78 daga cikin 127 da aka tsara, a cikin ƙananan hukumomi 11, abin da ke nuna ci gaba da daidaituwa tsakanin tawagar masu aikin.
Jama’a a wuraren da aka kai ziyara sun bayyana farin cikinsu da wannan shiri, suna ganin yana tabbatar da cewa gwamnati na kawo kiwon lafiya kyauta ga talakawa da marasa galihu ba tare da nuna bambanci ba.
Mai garin Kafinga a ƙaramar hukumar Rimin Gado,Alhaji Dauda Ado Bala, ya bayyana godiya ga gwamnati bisa wannan kokari:
“Muna matuƙar farin ciki da wannan shiri na BHCPF domin yana kawo kiwon lafiya kyauta kai tsaye ga jama’armu. Zuwa da KSCHMA take yi gidajenmu domin tabbatar da rajistar mu alama ce cewa gwamnati na kula da lafiyarmu. Muna yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’a, Allah ya ba shi ikon ci gaba da irin wannan aiki na alheri.”
Hukumar KSCHMA ta yaba da hadin kai daga Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA), hukumomin lafiya na ƙananan hukumomi, Kwamitocin Ci gaban Unguwanni (WDCs), da shugabannin al’umma da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar aikin.
A ƙarshe, hukumar ta bayyana cewa wannan matakin tantancewar Phase IV zai ƙunshi gundumomi 1,822 a cikin mazabu 127, da nufin tabbatar da mutane 46,013 da ke cin gajiyar shirin BHCPF, wanda ke baiwa marasa galihu damar samun kiwon lafiya kyauta a fadin Jihar Kano.

